Mutane 23 sun rasa rayukansu sakamakon rushewar wani gini da suka fake sakamakon ruwan saman da aka fara a lokacin halartar taron jana'iza a garin Gaziabad da ke jihar Uttar Pradesh ta Indiya.
Jaridun Indiya sun bayar da labarin cewa, mutane 38 sun kasance a karkashin ginin da mahalartar taron jana'izar suka fake saboda ruwan sama.
Ma'aikatan ceto sun ciro jikkunan mutane 23, wadanda kuma suka jikkata an kai su zuwa asibitocin yankin.
Ana ci gaba da gudanar da bincike kan afkuwar al'amarin.