Mutane 20 sun rasa rayukansu a filin jirgin saman Kabul dake Afghanistan

Mutane 20 sun rasa rayukansu a filin jirgin saman Kabul dake Afghanistan

A yayin ayyukan kwashe mutane da ake gudanar wa a filin tashi da saukar jirgin sama da ke Kabul, babban birnin Afghanistan, akalla mutane 20 sun rasa rayukansu a makon da ya gabata.

Bayan da 'yan Taliban suka karbe ikon Afghanistan, wadanda ke son barin kasar sun nufi filin jirgin saman Kabul.

Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters, wani jami’in kungiyar tsaro ta NATO ya ba da rahoton cewa akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a ciki da wajen filin jirgin saman a cikin kwanaki 7 da suka gabata.

Jami'in wanda ba a bayyana ko waye ba ya kara da cewa,

"Halin da ke wajen filin jirgin saman Kabul ba shi da kyau. Mu kuma mun mai da hankali ne kan kwashe dukkan baki 'yan kasashen waje cikin gaggawa." 

Jami'in ya kuma bayyana cewa dakarun NATO sun bayar da tazara mai nisan gaske a wajen filin jirgin sama domin kaucewa duk wata arangama da Taliban.


News Source:   ()