Mutane biyu sun rasa rayukansu a cikin bala'i da hadurra da suka afku sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a Islamabad, babban birnin Pakistan.
A cewar rahotannin jaridun kasar Pakistan, ambaliyar ruwa ta afku ne a bangarorin E-11 da D-12 na birnin sakamakon ruwan sama da ya fara da daddare kuma ya kara karfi a hankali tare da cika gidaje da wuraren kasuwanci da yawa.
Jami'an 'yan sanda sun sanar da cewa wata uwa da danta sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar a wani gida da ke kasan bene a bangaren E-11.
Mahukunta sun nemi 'yan ƙasa da su yi hankali kuma su dauki matakan kariya a yankin.
A cikin hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta, an ga cewa ambaliyar na tafiya da motoci.
Bayan ruwan saman wanda ya ragu da safiya, an fara aikin tsabtace wuraren da ambaliyar ta yi tasiri. Mambobin rundunar sojoji suma sun ba da tallafi a wannan kokarin.
Ruwan sama a Kudancin Asiya tsakanin watannin Yuni da Satumba na haifar da manyan bala'o'i da hadurra a kowace shekara.