Mutane 27 ne suka mutu yayin afkuwar walkiya da tsawa a gabashin Indiya.
A cewar labaran jaridun kasar, Ministan Kula da Bala'i na Yammacin Bengal, Javed Ahmed Khan ya ba da rahoton cewa walƙiya ta faɗa kan manoma da ma'aikatan fili a sassa daban-daban na jihar inda ake samun ruwan sama da hadari sosai.
Khan ya ce mutane 27 ne suka mutu yayin afkuwar walkiya da tsawa a garuruwan Hooghly, Murshidabad, Mindapore, Bankura da Nadia.
Kimanin mutane dubu 2 da 900 ne suka mutu a Indiya a shekarar 2019 sakamakon afkuwar walkiya da tsawa.