Mutane 17 ne suka mutu sakamakon rushewar gidan otel a China

Mutane 17 ne suka mutu sakamakon rushewar gidan otel a China

Ya zuwa yanzu mutane 17 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon rushewar wani gidan otel a China.

A garin Sujuo na jihar Jiangsu ne otel din ya rushe a ranar 12 ga Yuli.

An kawo karshen aiyukan ceto a wajen.

Mahukuntan garin Sujuon sun shaida cewa, mutane 17 ne suka mutu daga cikin 23 da aka ciro daga karkashin buraguzan ginin.

A shekarar 2018 aka bude gidan otel din mai dakuna 54.


News Source:   ()