A Yaman, mutane 14 ne suka mutu sakamakon harin makami mai linzami da 'yan Houthi masu samun goyon bayan Iran suka kai kan wani gidan man fetur a garin Marib.
A cikin sanarwar da aka fitar ta shafin Twitter din gwamnan Marib an bayyana cewa ‘yan Houthi sun kai harin makami mai linzami kan gidan man fetur da ke yankin matsugunan fararen hula a er-Ravda da ke arewacin birnin.
A cikin sanarwar an bayyana cewa fararen hula 14 ciki har da yara sun rasa rayukansu sannan da dama sun jikkata a harin, kuma an bayyana cewa an samu barna a yankin da ke kusa da ita.
’Yan Houthi ba su fitar da wani bayani game da harin ba.