Adadin mutanen da ambaliyar ruwan da mamakon ruwan sama ya janyo a kasar Bangaladash ya kai mutane 119.
Sanarwar da gwamnatin Bangaladash ta fitar ta ce a awanni 24 da suka gabata mutane 8 sun sake rasa rayukansu.
Sanarwar ta ce daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa yau adadin wadanda suka mutu sakamakon ibtila'in sun kai mutane 119, kuma a yankuna 21 daga cikin 64 na kasar mutane dubu 10,684 sun samu raunuka.
Sanarwar ta kara da cewar kusan mutane dubu 5 sun kamu da amai da gudawa sakamakon ruwan sha mara kyau da suka sha a yankunan da ambaliyar ta shafa.