Mutane 119 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar kasar da mamakon ruwan sama ya janyo a jihar Assam da ke Indiya.
Labaran da jaridar Press Trust of India ta fitar sun rawaito Hukumar Magance Annoba ta jihar Assam na cewar ambaliyar da ta yi ajalin mutane 119 ta illata mutane miliyan 2.8.
Kauyuka sama da dubu 2,500 sun samu matsala, kuma an samar da sansanoni sama da 28 don tsugunar da wadanda ambaliyar ta raba da gidajensu.
Gadoji, hanyoyi da magudanan ruwa sun samu matsala tare da lalacewa a jihar.
Ana ci gaba da aiyukan ceto a yankunan da ibtila'in ya shafa.