Mutane 10 sun rasa rayukansu sakamakon hari da bindiga da aka kai a wani kanti da ke jihar Colorado ta Amurka.
Sashen 'Yan sandan Boulder ya shaida cewa, adadin mutanen da aka kashe a harin da aka kai a Babban Kantin Boulder ya tashi zuwa mutane 10.
Dan sanda 1 ya mutu sakamakon bude wuta da maharin ya yi a lokacin da 'yan sanda suka je wajen.
Mahukunta sun fara gudanar da bincike game da harin.
An kama maharin da ya samu raunuka a jikin sa. Ba a bayyana waye maharin ba.