Musulmi na farko zai zama Babban Jojin Tarayya a Amurka

Musulmi na farko zai zama Babban Jojin Tarayya a Amurka

Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya mika sunan Zahid Kuraishi dan asalin Pakistan ga Majalisar Dattawa don ta amince da shi a matsayin Babban Alkalin Kotun Tarayya.

Idan Kuraishi ya samu amincewar Majalisar Dattawa, zai zama Musulmi na farko da ya zama Alkali a Kotun Tarayya ta Amurka.

Biden da ya hau kan mulki a ranar 20 ga Janairun 2021, ya bayyana sunayen mutane 11 da ya ke son su zama Manyan Alkalan Tarayya na Amurka.

Biden ya bayar da sunayen mata 'yan asalin Afirka 3 tare da Zahid Kuraishi dan asalin Pakistan a matsayin Alkalan Kotunan Tarayya na yankin New Jersey.

 


News Source:   ()