An sanar da bulluwar murar tsuntsaye a wani gidan gonan dake yankin Cheshire a kasar Birtaniya.
A gidan gonan an kashe tsuntsaye har dubu 4 da 500 sanadiyar kamuwa da murar.
A yayinda aka kange gidan gonan an kuma dauki matakan dakile yaduwar murar tsuntsaye a yankin.
Maaikatan gidan gonan ne suka lura da cewa tsuntsayen gidan gonan basu da lafiya.
Lamarin ya sanya yin gwaje gwaje akan tsuntsayen inda aka gano cewa suna fama da mura.
Hukumomin lafiyar kasar Birtaniya sun bayyana cewa murnar tsuntsayen da wuya ta shafi bil adama kuma ba ta da alaka da annobar Korona virus.
Akwai de gidaje kimanin dubu 200 zuwa dubu 300 a yankin da aka samu barkewar murar tsuntsayen.