Bayan barkewar cutar murar tsuntsaye a Afirka ta Kudu, kasashe 3 sun hana shigo da kayayyakin kaji daga kasar.
Kamar yadda jaridun kasar suka sanar, kasashen dake makwabtaka da Afirka ta Kudu sun firgita bayan da Kungiyar Kaji ta kasar ta sanar da cewa dabbobi 300 a wata gonar kaji sun mutu daga murar tsuntsaye.
Botswana, Namibia da Mozambique sun hana shigo da dukkan kayayyakin kaji da suka hada da kwai da namansu.
An bayyana cewa, an kebe gonar da ke cikin garin Ekurhuleni, inda annobar ta faru.
Irin wannan annoba ta faru a kasar a cikin 2017 a lokacin da aka kashe miliyoyin tsuntsaye.