An sanar da yiwuwar afkuwar annoba a Indiya sakamakon bullar murar tsuntsaye.
Ma'aikatar Muhalli ta sanar da cewar, an samu bullar cutar H5N8 a jihohi 5 na kasar, kuma hakan ya sanya daukan matakan kar ta kwana.
Ma'aikatar ta bukaci jihohin da su dauki matakan da suka dace don kar cutar ta kama dabbobin da yawa.
Mahukuntan garin Panchkula na jihar Haryana sun bayyana cewar an kashe tsuntsaye dubu 350 da suka kamu da cutar a garin.
A jihar Himachal Pradesh kuma an bayyana mutuwar agwagi da suka yi hijura zuwa yanki su sama da dubu 2,400 sakamakon kamuwa da cutar ta H5N8.