Murar tsuntsaye ta bulla a Faransa

Murar tsuntsaye ta bulla a Faransa

An bayyana za a kashe kaji da tsuntsaye dubu 600 a kudu maso-yammacin Faransa sakamakon bullar murar tsuntsaye.

Ma'aikatar Noma da Kiwo ta sanar da cewa, ya zuwa yanzu an kashe sama da tsuntsaye dubu 200 a yankin.

A shekarar da ta gabata an kashe tsuntsaye dubunnan daruruwan tsuntsaye a Faransa sakamakon bullar murar tsuntsayen.

Ma'aikatar ta sanar da cewar, daga 1 ga Janairu cutar murar tsuntsaye ta H5N8 ta bulla a yankuna 61 na kasar.

Cutar murar tsuntsaye ta H5N8 ba ta kama mutane.


News Source:   ()