A lokacin da Indiya ka fama da annobar Corona, a gefe guda kuma guguwa na addabar kasar. A jihar Bihar da Ibtila'in ya fi shafa gidaje da asibitoci sun kasance a karkashin ruwa.
Indiya da ta kasance daya daga cikin kasashen da Corona ta fi illatawa a duniya na fuskantar ibtila'in guguwa a jejjere.
Guguwar Yaas da ta kunna kai jihar Bihar ta janyo ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama.
A jihar da annoba ta janyo matsala sosai, gidaje sun kasance a karkashin ruwa.
Asibiti da Sashen Koyon Likitanci na Darbhanga na daga wuraren da ruwa ya mamaye.
Lamarin ya sake munana a lokacin da masu fama da Corona suka tsinci kawunansu a cikin ruwa makil. An kwashe a kalla mutane miliyan 1 daga gidajensu a yankunan da guguwar ta yi karfi.