Sojoji 2 da 'Yan tawaye 40 sun rasa rayukansu sakamakon arangamar da aka yi a garin Hudeyde na Yaman tsakanin dakarun gwamnatin mayakan Houthi 'yan Shi'a.
Kakakin dakarun Amalika mai alaka da Rundunar Sojin Yaman, Mamnun Al-Mahjami ya shaida cewa, 'yan tawayen Houthi sun yi kokarin shiga yankin kudancin Hudeyde da ke hannun dakarun gwamnati.
Sanarwar ta kara da cewa, a arangamar da aka yi da Houthi, an kashe 'yan tawaye 40 tare da jikkata wasu 55. Haka zalika sojoji 2 sun mutu yayinda wasu 10 suka jikkata.
Hare-Haren da mayakan Houthi su ke kaiwa a Hudayde, na lalata yunkurin Majalisar Dinkin Duniya na samar da zaman lafiya a yankin.