Mummunan hatsarin mota a Bolibiya

Mummunan hatsarin mota a Bolibiya

Mutane 21 sun rasa rayukansu, wasu 20 sun jikkata sakamakon juyin wainar da wata motar bas ta yi a kasar Bolibiya da ke nahiyar Amurka ta Kudu.

Labaran da jaridun Bolibiya suka fitar sun ce, motar bas din dauke da fasinjoji daga garin Cochabamba na tsakiyar kasar zuwa Cruz, ta yi juyin waina a kauyen Calomi sakamakon rasa iko da sitiyarinta da direba ya yi.

Mahukuntan kasar sun ce, a kalla mutane 21 ne suka mutu, wasu 20 kuma suka samu raunuka.

Daya daga cikin fasinjojin da suka jikkata a hatsarin mai suna Erwin Tumiri na daga cikin 'yan wasan kwallon kafar Barazil da suka kubuta da rayuwarsu sakamakon hatsarin jirgin sama a ranar 29 ga watan Nuwamban 2016 a Kolombiya.

Tumiri da ya dan samu rauni a bayansa da cinyarsa ya godewa Ubangijinsa sakamakon kasancewa a raye a karo na 2.

A hatsarin jirgin sama dauke da 'yan wasan kwallon kafa na Barazil su 81, mutane 5 ne kawai suka tsira da rayuwarsu.


News Source:   ()