Mutane 30 sun rasa rayukansu, wasu 50 sun jikkata sakamakon hatsarin jirgin kasa da ya afku a jihar Sindh ta Pakistan.
Mahukunta sun bayyana cewa, taragon wani jirgin kasa da ke tafiya a yankin Gotki na jihar ne ya karye tare da cin karo da wani jirgin kasa da ke tahowa daga daya bangaren.
Rahotannin farko da aka fitar sun bayyana mutuwar mutane 30 tare da jikkatar wasu 50 sakamakon hatsarin, ana kuma ci gaba da aiyukan ceto.