Hukumomi a Ukraine sun tabbatar da cewa harin makami mai linzami da Rasha ta kai ya shafi wani Otal tare da hallaka mutane 2 a tsakiyar Kryvyi Rih, har ila yau harin ya kashe mutum 3 a Zaporizhzhia.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya ce zasu mayar da martani kan harin na Rasha, inda ya bukaci kasashen da suke ɗasawa su amince da aikin tsaron sararin samaniya na haɗin gwiwa da kuma bada damar amfani da makamai masu nisan zango biyo bayan harin makamai masu linzami sama da 200 na ranar litinin da aka kaiwa ƙasarsa.
A ranar talata kuwa hukumomin Ukraine sun tabbatar da kakkaɓo makamai masu linzami 5 cikin 10 da Rasha ta harba, tare da daƙile harin jirgi maras matuƙi 60 ciki 81 da aka kawo musu.
Kamfanin dillancin labarai na Interfax ya rawaito ministan tsaron Rasha na cewa sun kaiwa Ukraine mummunan hari ta sama da tsakar dare, amma ya musanta hallaka fararen hula tun daga lokacin da suka kutsa Ukraine a Fabarairun 2022, dukda rahotanni na tabbatar da an hallaka dubban mutane a yaƙin.
Masu wallafa bayanai na sojin Rasha sun ce harin da Mascow ke kaiwa Ukraine na ramuwa ne saboda kutsawar da ta yi zuwa kudancin Kurst dake Rasha
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI