A Misira mutane 12 da suka hada da yara sun mutu sakamakon kifewar motar fasinja.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Masar na MENA ya bayar, motar fasinja ta kife a kan babbar hanyar Alkahira zuwa Suez dake gabashin kasar.
A cikin hadarin mutane 12 da suka hada da yara sun rasa rayukansu yayin da 34 suka jikkata.
A halin da ake ciki Turkiyya ta fitar da sakon ta'aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu a hadarin mota.
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta fitar an bayyana cewa,
"Muna fatan Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin, muna kuma fatan samun saukin wadanda suka jikkata cikin dan kankanen lokaci"