Mujallar sojin Amurka ta jinjinawa Ataturk

Mujallar sojin Amurka ta jinjinawa Ataturk

Mujallar sojojin kasar Amurka wato Military Review ta yabi da jinjinawa shugabancin wanda ya kafa jamhoriyyar Turkiyya Mustafa Kemal Ataturk.

Mujalllar da sanya hannun Manjo Eric Venditti ta yi babban yabo ga namijin kokarin da wanda ya kafa jamhoriyyar Turkiyya wato Ataturk ya yi a lokacin yakin Canakkale a shekarar 1915.

Mujallar ta bayyana cewa ya dauki shawarar da ta dace a wajajen yakin.

A kasidar, an bayyana cewa Mustafa Kemal ya ba wa sojojinsa wata kyakkyawar alkibla da kuma kwarin gwiwa don daukar mataki, inda ya ke ce musu "Na umurce ku da ku mutu, ba hari ba".

Labarin ya yi cikakken bayani game da dabarun soja a yakin Canakkale; An jaddada cewa shugabancin Kemal  da jagorancinsa ya kamasance mai alfano duk da bayan sama da karni.

 


News Source:   ()