Muhimman batutuwan da suka shafi yaƙin Gaza

Muhimman batutuwan da suka shafi yaƙin Gaza

Abin da ya faru a wannan rana shi ne, wani gagarumin farmaki da mayakan Hamas suka ƙaddamar daga Gaza a kan wurare da dama cikin Isra’ila, ciki har da wurin da ake gudanar da ɗaya daga cikin muhimman bukukuwan da Yahudawa ke gudanarwa a kowace shekara.

An yi amfani da makamai masu linzame, da rokoki, da sojin ƙasa da kuma wasu kananan babura masu fikafikai da ke tashi sama, ɗauke da mutane masu makamai da suka rika dira a cikin Isra’ila.

Ana iya cewa wannan farmaki ne da Hamas ta jima tana tsarawa ba tare da cewa ita Isra’ila ta ankara ba, domin kuwa kafin hukumomin tsaron Isra’ila su iya mayar da martani, tuni maharan suka kashe akalla Yahudawa dubu daya da 200, sannan kuma suka yi garkuwa da akalla wasu mutanen 250.

To ko ana iya cewa an kai hare-haren ne a cikin yanayi na ba-zata?

Tabbas, ya zo wa wasu a cikin yanayi na ba-zata, yayin da wasu ke ganin cewa ba wata ba-zata idan aka yi la’akari da tsawon shekarun da aka share ana zaman doya-da-manja tsakanin Isra’ila da al’ummar Falasdinu.

Wane ɓangare na gine-ginen da aka rusa a Gaza Wane ɓangare na gine-ginen da aka rusa a Gaza © 路透社 - Mahmoud Issa摄影

Abu na biyu, idan aka aka yi la’akari da kasancewar yankin Gaza a karkashin mamayar Isra’ila, amma kuma mayakan na Hamas suka yi nasarar tsara wannan mummunan hari, a nan, ana iya cewa an samu gazawa daga ɓangaren tsaro da kuma tara bayanan sirri na Isra’ila da na kasashen da ke taimaka ma ta ta fannin tsaro.

To an jima ana fama da rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, shin ko akwai wani bambanci tsakanin wannan rikici da kuma wadannan da suka gabace shi?

Akwai abubuwa da dama da suka bambanta su, na farko idan aka yi dubi a game da girman hare-haren da Hamas ta kai a wannan rana ta 7 ga watan oktoba, da kuma zazzafan martanin da Isra’ila ta mayar akan al’ummar da ke zirin Gaza ciki har da sansanonin ‘yan gudun hijira, asibitoci, makarantu da dai sauransu.

Wata uwa da ta rasa ɗanta a yaƙin Gaza Wata uwa da ta rasa ɗanta a yaƙin Gaza AP - Abdel Kareem Hana

Wani abu game da wannan rikici shi ne, yadda aka jingine batun kare haƙƙin ɗan Adam, domin kuwa a rana ɗaya Isra’ila ta taɓa bai wa mutane sama da milyan ɗaya da rabi umurnin tashi daga yankin Arewaci zuwa Kudancin Gaza, bayan kwanaki kaɗan kuma, sai ta ba su umurnin cewa su sake tashi daga kudu zuwa arewa, ba ruwa, ba wuta, ba motocin sufuri, ba muhalli balantana sha’anin kiwon lafiya.

To yaya za a bayyana girman ɓarnar da wannan yaƙi ya haddasa a cikin shekara ɗaya?

Lalle, an kashe mutane masu tarin yawa a cikin shekara daya: kamar yadda na faɗa tun da farko, an kashe Yahudawan Isra’ila kusan dubu 1 da 200 tun a ranar 7 ga watan oktoban bara, Palasdinawa kuwa, kawo yanzu an kashe kusan dubu 42, yayin da a Libanan kuwa aka kashe sama da mutane dubu 2 a cikin makonni biyu.

Sojojin Isra'ila a Lebanon Sojojin Isra'ila a Lebanon © Baz Ratner / AP

Ba shi kenan ba, domin kuwa rikicin ya yi sanadiyyar lalata gidajen sama da mutane milyan uku da ke zaune a Gaza, waɗanda a yau suke rayuwa a kan titi ko kuma a sansanonin ‘yan gudun hijira, kuma akwai wasu dubbai da suka rasa muhallansu a kasar Libanan.

To a yau, ko akwai wani tasiri da wannan yaki ya yi wa zamantakewar al’ummar duniya?

Ko ba komai dai ana iya cewa wannan rikici, ya ƙara fitowa fili da rashin adalci dangane da yadda ake tafiyar da siyasar duniya, sannan kuma ya ƙara fitowa fili da gazawar manyan ƙasashe da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin warware wannan daɗaɗɗen rikici na yankin Gabas ta Tsakiya.

Ƙungiyar Kashen Larabawa ta yi tir da hare haren Isra'ila a Lebanon. Ƙungiyar Kashen Larabawa ta yi tir da hare haren Isra'ila a Lebanon. REUTERS - RAMZI BOUDINA

Hakazalika, 7 ga watan oktoba da kuma abubuwan da suka biyo baya, sun ƙara fitowa fili ƙarara cewa, ƙasashen Larabawa, wato a ƙungiyance ba wai a ɗaiɗaiku ba, sam ba su damu da abin da ke faruwa ba a yankin ba.

Hujjar faɗar hakan kuwa ita ce, tsawon shekara ɗaya, ƙungiyarsu (ta Arab League) ta gaza gudanar da taro balantana ma ta ce wani abu a game da wannan lamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)