Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da ECOWAS din ta fitar, tana mai cewa har yanzu kofa a bude take ga wadannan kasashe, a duk lokacin da suka sauya shawarar sake koma wa.
Matakin farko dai ECOWAS ta ce tsare-tsare ko dokokin da suka shafi makomar cuɗanyar ƴan kasashen da suka fice daga cikinta da kuma na kasashen manbobinta, da suka hada da izinin zama domin aiki, mallakar kamfanoni, shige da fice ba tare da biza ko fasfo ba za su ci gaba da wanzuwa kamar yadda suke a baya, har zuwa lokacin da shugabannin kasashen ECOWAS za su gana da tsara yadda makomar sabuwar alaƙarsu za ta kasance.
ECOWAS ta kuma sake yi wa kasashen na AES ranngwame ta hanyar kara msusu wa’adin watanni shidda na basu damar sauya shawarar ficewar da suka yi.
Ficewar AES daga ECOWAS
Abinda zai biyo bayan ficewarsu dangane da shige da fice musamman kan bukatar fasfo da kuma yadda hakan zai shafi kai kawo jama’a da kayayyaki ciki har da fuskar kasuwanci
Menene makomar takardun kudiin da suek amfani da su na CFA, la’akari da cewar har yanzu bayanai na nuna da Faransar da suka yanke alalaka da itan ce dai ke cigaba da buga musu takardun kudi.
So abin ttambaya anan shi ne
Shin za su ci gaba da mafanin da wannan CFA ne? Ko kuma za su buga nasu takardun kudin kamar yadda suka taba ambatawa a baya?
Idan sun aiwatar da hakan yaya darajar kudin za ta kasance? Wace kariya za su bashi idan suka samar da kudin na bai daya nan da shekarar 2027?
Wani batu kuma shi ne daga cikin manyan dalilan da suka janyo sauyi na juyin mulkin sojoji a waɗannan ƙasashe na AES da suka haɗa da Nijar da Burkina Faso da kuma Mali da ya kai ga ficewarsu daga ECOWAS bayan katse dukkanin alaƙa tsakaninsu da kasashen yammacin Turai ciki har da tsohuwar uwargijiyarsu Faransa, shi ne zargin kasashen da gazawa wajen cika alƙawurran taimaka musu ta fuskar tsaro da bunƙasar tattalin arziƙi da dai sauran fannoni, inda a maimakon haka suka zarge su da azurta kansu da tarin arzikin da su ƙasashen suka mallaka.
Waɗannan ƙasashe guda uku na AES sun karkata sosai wajen kulla alaka da Rasha tun kafin raba gari da aka yi tsakaninsu da ƙasashen Turan ciki har da Faransa da kuma ECOWAS.
Wannan ya sa wasu daga cikin masana tambayar makomar sabuwar alaƙar da suka ƙulla da Rasha? Wane hali ake ciki? Ta wace hanya za a cike gibin kudaden tallafin da kasashen na AES ke samu a baya? Waye zai cike gibin kuma? Sannan wace sabuwar alkibila za su samawa ginshikin tattalin arzikinsu.
Da wannan batu ne kuma lamarin haraji zai bijiro domin ficewar ƙasashen uku zai sanya su daina amfana da tsari kasuwanci na bai daya tsakaninsu da sauran takwarorinsu na kasashen yammacin Afirka, zai yi wahala ba a sanya wa kayayyakinsu haraji ba, uwa uba kuma shi ne babu ɗaya daga cikinsu da ke da gabar ruwa ko tashar jiragen dakon kaya, shi ma nan wani sabon kalubalen ne.
Ƙarfin tattalin arzikin ƙasashen AES da kuma asarar da za su yi idan suka fice daga ECOWAS
Da farko dai ficewar ƙasashen AES daga ECOWAS na nufin sun daina amfana da romon albarkatun Bankin Zuba Hannayen Jari da kuma bunƙasa ci gaban ƙasashen yammacin Afrika na ECOWAS EBID.
A takaice dai ƙasashen na Nijar, Mali da Burkina Faso za su rasa amfana da zuba hannun jarin kuɗaɗen da yawansu ya kai akalla dala miliyan 500, sakamakon matakinsu na ficewa daga ECOWAS.
Yaya karfin tattalin arzikin kasashen AES yake?
Ko shakka babu waɗannan ƙasashe na da karfin tattalin arziki matuka, wanda kuma za su iya dogara akai, ga misali, Jamhuriyar Nijar na da arzikin ɗanyen man fetur da makamshin Uranium da ke taka rawa wajen samar da karfin hasken latarkin mai karfi da rahusa, da kuma uwa Uba makamai da manyan kasashe ke tsananin bukata.
Ita kuwa Mali A ya horewa kasar dimbin arziki ne na ma’adanin Lithium, wanda ake tsananin bukatarsa a duniya wajen sarrafawa ko samar da kayayyaki masu alaka da lantarki da kuma batura. Yayin da Burkina Faso ta mallaki arzikin Zinare.
Wannan arziki da kasashen uku suka mallaka idan har suka yi amfani da shi wajen kafa nasu bankin da zai taka rawa wajen bunkasar tattalin arzikinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI