Muhammad Yunus shugaban gwamnatin rikon kwaryar Bangladesh ya isa kasar

Muhammad Yunus shugaban gwamnatin rikon kwaryar Bangladesh ya isa kasar

Yunus ya lashe kyautar lambar yabo a shekarar 2006 saboda rawar da ya taka wajen kawar da matsanancin talauci a Bangladesh ta hanyar ba wa dubun dubatar mata kudaden rance musaman a yankunan karkara, ta hannun bankinsa na Grameen, wanda ya lashe kyautar Nobel.

Yunus  a wancan lokaci y ana mai bayyana cewa ‘ba a haifi ’yan Adam don fama da kunci, yunwa da talauci ba.”

Bayan wannan banbance-banbance, sai ya yi la’akari da kafa jam’iyya kafin ya yi gaggawar barin aikin nasa.

 Muhammad Yunus,a filin tashin jirage na Faransa Muhammad Yunus,a filin tashin jirage na Faransa REUTERS - Abdul Saboor

 Amma duk da haka ya jawo kiyayyar wani bangare na masu mulki, inda tsohuwar Firaminista  Hasina ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen zargin shi da "shanye jinin" talakawa. Muhammad Yunus wanda ake tuhumarsa da aikata laifuka sama da 100, ya yanke shawarar tafiya gudun hijira bayan da aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida a watan Janairu bisa laifin keta dokar aiki. Kotun daukaka kara ta wanke shi a ranar Laraba.

 Tsohuwar Firaministar kasar Hasina ta gudu ne a ranar litini sakamakon matsin lamba daga masu bore saman titunan wannan kasa bayan shafe shekaru 15 ta na jagorantar wannan kasa.

Masu zanga-zanga a Bangladesh Masu zanga-zanga a Bangladesh AP - Rajib Dhar

 Shugabannin daliban da suka gudanar da zanga-zangar, wadanda zanga-zangarsu ta kai ga korar shugaban, sun ce suna son Muhammad Yunus ya jagoranci gwamnatin wucin gadi.

A karshe dai an dauki matakin kafa irin wannan gwamnati ne a wata ganawa tsakanin shugaban kasa Mohammed Shahabuddin da manyan hafsoshin soji da kuma shugabannin kungiyar daliban da ke yaki da wariyar launin fata, wanda shi ne babban yunkurin da aka fara gudanar da zanga-zangar a farkon watan Yuli, kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar a jiya Laraba.

A wata rubutacciyar sanarwa ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP jim kadan kafin dawowarsa, Yunus ya na mai kira da a shirya "sahihin zabe da kuma baiwa jama’a damar zabar abinda suke so cikin  'yanci".

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)