Muftin Kudus da Falasdin Sheik Muhammed Hüseyin, ya yi garagdi da ja kunnen Isra’ila game hatsarin kirar da suka yi na kai mamaye a Masjid al-Aqsa a ranar bikin babban sallah 30 ga watan Yulin.
Sheik Muhammed Hüseyin a sanarwar da ya fitar a rubuce ya yi kira ga dukkanin Falasdinawa da su bayyana a Masjidul al Aqsa a ranar domin kalubalantar matakin na Isra’ila.
Mufti Hussain ya kara da cewa kirar kungiyoyin Yahudawa da masu ra’ayin tada zaune tsaye suka yi na a kai mamaye a masjid Aksa lamari ne dake nuna kalubalantar imanin al’umman Musulmin duniya baki daya.