Muddin kasar Iran ta hallaka ni, Amurka zata share ta daga doran kasa - Trump

Muddin kasar Iran ta hallaka ni, Amurka zata share ta daga doran kasa - Trump

Trump ya yi wadannan kalamai ne a cikin wani gajerin bidiyo wanda ya yi daidai lokacin jawabin  firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a majalisar dokokin kasar, abinda ke dada fito da barazanar shirin da kasar ke yi a kan tsohon shugaban na Amurka.

Kafofin yada labaran Amurka a makon jiya sun bayyana cewar an sake tsaurara tsaron da ake bai wa Trump tun makwannin baya, lokacin da hukumomin kasar suka samu bayanan asiri dake nuna yunkurin hallaka shi, duk da yake ba'a danganta shi da harin da wani matashi 'dan shekaru 20 ya kai wajen harbin tsohon shugaban ba.

Kafar yada labaran CNN tace hukumomin Amurka sun samu bayanan ne daga wani mutum dangane da barazanar na Iran, abinda ya sa nan take aka kara yawan masu tsaron sa.

Sai dai hakan bai hana harbin da Thomas Mathew Crooks, 'dan Amurka ya masa ba, inda ya masa rauni a kunnen.

Dangantaka tsakanin Amurka da Iran ta dade da yin tsami, yayin da Iran ke tunanin daukar fansa dangane da kisan gillar da Amurkar ta yiwa kwamandan zaratan sojin ta Qasem Soleimani a shekarar 2020.

Majalisar tsaron Amurka tace ta dade tana bin diddigin barazanar da Iran ke yiwa tsohon shugaba Donald Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)