Mu muka kai hari kan gidan Netanyahu - Hezbollah

Mu muka kai hari kan gidan Netanyahu - Hezbollah

Mai magana da yawun Hezbollah, Mohammed Afifi ya bayyana haka a yayin wani taron manema labarai a kudancin birnin Beirut.

Jim kaɗan da kammala taron manema labaran ne, Isra'ila ta kai hari a kusa da zauren taron bayan ƴan jarida sun fice  kamar yadda wani ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP

A raanar Asabar da ta gabata ne, Netanyahu ya zarfi Hezbollah da yunƙurin halaka shi da matarsa bayan harbo wani jirgi mara matuƙi kan gidansa da ke tsakiyar birnin Caesarea. 

Afif ta kuma ce, Isra'ila ta kama musu wasu daga cikin mayaƙansu ba tare da ya faɗi adadinsu ba.

A can baya, rundunar Isra'ila ta yi iƙirarin kama mayaƙan Hezbollah huɗu tun bayan da ta fara kai hari cikin Lebanon ta ƙasa, inda har ta saki wani hoton bidiyo da ke nuna yadda take yi wa ɗaya daga cikin mayaƙan na Hezbollah tambayoyi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)