Ministan tsaron kasar Turkiyya Hulusi Akar da ministan harkokin waje Mevlut Cavusoglu sun tattauna akan sabbin abubuwan da suka faru a Afghanistan da takwarorinsu na Katar.
Dangane da bayanin da Ma'aikatar Tsaro ta Kasar Turkiyya ta fitar, Ministan Tsaron Kasa Akar da Ministan Harkokin Waje Cavusoglu sun yi ganawar bidiyo ta wayar tarho tare da Ministan Harkokin Wajen Katar Mohammed bin Abdurrahman Al Sani da Ministan Tsaron Katar Khalid bin Muhammed al -Atiye.
A yayin taron, an ba da rahoton cewa an tattauna sabbin abubuwan da suka faru a Afghanistan.