Ministocin harkokin ƙasashen wajen G20 sun gana kan batun kasuwanci da yaƙin Ukraine

Ministocin harkokin ƙasashen wajen G20 sun gana kan batun kasuwanci da yaƙin Ukraine

Kafin wannan taron Kasashen 20, wadanda ke riƙe da kusan kashi 85% na ƙarfin tattalin arzikin duniya tare da mamaye kaso uku bisa huɗu na cinikayya a faɗin duniya, basu fiya jituwa dari bisa ɗari ba, sai dai matsalar rarrabuwar kansu ta ƙara bayyana tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.

Lamura sun sake dagule wa bayan matsalar da ake ciki tun bayan da shugaba Donald Trump na Amurka ya sake ɗarewa karagar mulki a watan jiya, inda ya sauya mafofin ƙasar na ƙasashen ketare da suka shafi diflomasiya da kuma kasuwanci.

Afirka ta kudu na kallon taron na G20 wanda shine karo na farko dake gudana a nahiyar Afirka a matsayin wata gwaggwaɓar dama, da zai sanya ƙasashen masu arziki mayar da hankali wajen taimakawa ƙasashe marasa ƙarfi, lura da zaman kashin dankalin da ake yi tsakaninsu, musamman ta fuskar yaki da matsalar sauyin yanayi da kuma hada-hadar ƙarfafa tattalin arziƙinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)