Ministan harkokin tsaron kasar Turkiyya Hulusi Akar ya tattauna da takwaransa na Libiya Selahaddin Nemrush a birnin Istanbul.
Kamar yadda ma'aikatan tsaron kasar Turkiyya ta sanar, a tattuanawar ministocin biyu an aminta akan aiki tare da karfafa lamurran tsaro tsakanin kasashen biyu.
Minista Akar, ya tabbatar da cewa Turkiyya za ta cigaba da kasancewa da kuma bayar da goyon baya ga halastacciyar gwamnatin Libiya da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa.
Bugu da kari, minista Akar ya nanata matsayin Turkiyya na goyon bayan bin hanyar siyasa domin kawo karshen rikicin kasar Libiya baki daya.