Ministan tsaron Turkiyya ya tattauna da takwaransa na Amurka

Ministan tsaron Turkiyya ya tattauna da takwaransa na Amurka

Ministan tsaron kasar Turkiyya Hulusi Akar ya tattauna da takwaransa na Amurka  Lloyd Austin ta wayar tarho.

A cikin bayanin da Ma'aikatar Tsaro ta Kasar Turkiyya ta yi, an ruwaito cewa Akar da Austin sun tattauna ta wayar tarho.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa a yayin taron, wanda ya kasance mai kyau da ma'ana, an yi musayar ra'ayoyi kan lamuran tsaro da na yankin bayan taron kolin NATO.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa daga ofishin yada labarai na Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon, an lura cewa Lloyd da Akar sun yi magana game da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaba da kasancewar diflomasiyya a Afghanistan.

A cikin sanarwar, an bayyana cewa, Lloyd ya sake jaddada mahimmancin dangantakar tsaron Amurka da Turkiyya wacce ta dade kuma ya gode wa Akar kan ci gaba da hadaka da musayar bayanai da kasashen biyu ke cigaba da yi akan harkokin tsaro.
 


News Source:   ()