Ministan tsaron Libiya ya ja kunnen mayakan Haftar

Ministan tsaron Libiya ya ja kunnen mayakan Haftar

Ministan harkokin tsaron kasar Libiya ya ja kunnen mayakan Janar Khalifa Haftar akan shirin da suke yi na kai wani hari a kasar.

Minista Salah Eddine al-Namrush ya jaddada cewa mayakan Haftar na shirin kai hari a yankunan Bani Walid, Giryan daTarhuna .

Al-Namrush ya umarci kwamandojin yankin da su kasance cikin ko ta kwana domin kalubalantar dukkan wani harin da mayakan Haftar din zasu kai.

A bayanan da ya fitar da tweeter, al-Namrush ya kara da cewa sojojin gwamnatin Libiya da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa na mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta, amma hakan ba zai hanasu kai ramuwa ko mayar da martani ga ko wani irin harin da aka kai musu ba.


News Source:   ()