Ministan tsaron kasar Turkiyya na ziyara a Pakistan

Ministan tsaron kasar Turkiyya na ziyara a Pakistan

Ministan harkokin tsaron kasar Turkiyya Hulusi Akar dake ziyara a kasar Pakistan ya gana da ministan sarrafa kayayyakin tsaron kasar Zubaida Jalal Khan.

Ministan tsaron kasar Turkiyya Hulusi Akar ya ziyarci Pakinstan ne domin halartar bikin bude jirgi yaki kirar MILGEM da Turkiyya ta aikewa Pakistan.

Minista Akar gabanin halartar taron ya gana da ministan harkokin sarrafa kayan tsaron kasar Pakistan Zubaida Jalal Khan.

Ministocin biyu sun tattauna akan musayar bayanai da sarrafa kayayyakin tsaron hadin gwiwa da kuma wasu lamurkan da suka shafi yankunan baki daya.

 


News Source:   ()