Ministan Tsaron Isra'ila ya yi magana game da barazanar makaman nukiliyar Iran

Ministan Tsaron Isra'ila ya yi magana game da barazanar makaman nukiliyar Iran

Ministan Tsaron Isra’ila, Benny Gantz ya bayyana cewa mallakar makamin nukiliya da Iran ta yi shi ne babbar barazana ga kasarsa.

A cewar labarin a jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta rawaito, Gantz ya yi bayani a wurin bukin da aka gudanar a sansanin soja na Dayan da ke kusa da Tel Aviv.

Gantz ya lura cewa Isra’ila na fuskantar wasu matsaloli kuma Gabas ta Tsakiya ta samu sauyi na asali, Gantz ya lissafa wadannan kalubale a matsayin wargajewar Labanan, barazana daga Siriya da kuma rawar da Iran ke takawa a wadannan lamuran.

Tare da jaddada bukatar kasancewa cikin shiri dangane da barazanar, Gantz ya ce,

"Babbar barazanar da muke fuskanta ita ce yaduwar makaman nukiliyar Iran. Ba mu da wani zabi face kara karfi." 


News Source:   ()