Ministan Harkokin Kiwon Lafiyar Birtaniya Sajid Javid ya bayyana kamuwa da kwayar cutar Korona, sai dai alamun suna da sauki.
Sajid Javid ya sanar a shafukan sada zumunta cewa gwajin Kovid-19 da aka yi masa ya nuna ya na dauke da ita.
Javid ya bayyana cewa yana jiran sakamakon gwajin PCR don tabbatarwa.
"Abin godiya, alamun na masu sauki ne," in ji Javid, yana mai kara da cewa baya cikin mawuyacin hali.
Da yake tunatar da cewa ya yi allurai biyu na rigakafin cutar, Javid ya jaddada mahimmancin yin rigakafin.
Minista Javid ya ce "Idan har yanzu ba a yi muku allurar rigakafin ba, don Allah kuyi shi," in kowa ya yi nasa gudummawar, ba wai kawai za ku kare kanku da masoyanku ba, amma kuma za ku kare Hukumar Kiwon Lafiya ta Kasa.