Ministan kanfunan Sudan ya kamu da Korona

Ministan kanfunan Sudan ya kamu da Korona

Ministan harkokin kanfunan kasar Sudan Ibrahim al-Sheikh ya kamu da kwayar cutar Korona.

Al-Sheikh ya bayyana a shafinsa na Facebook da cewa baya ga shi matarsa da ‘yarsa ma sun kamu da Covid-19.

Ministan ya bayyana cewa gwajin da aka yi masa na farko ya nuna cewa ya kamu da cutar zazzabin cizon sauro ne amma daga baya bayan maganin Maleriya bai yi masa aiki ba aka yi masa gwajin Korona.

A kasar Sudan dai an samu mutum dubu 28,545 dauke da cutar ta Korona da kuma rasa rayukan mutane dubu 1,895 sakamakon kkamuwa da cutar.

A makon jiya kasar Sudan ta shigo da allurar riga-kafin Korona sanfarin AstraZeneca kwara dubu 820,000

 


News Source:   ()