“Miliyoyin mutane zasu fada cikin matsalar yunwa a doron kasa”

“Miliyoyin mutane zasu fada cikin matsalar yunwa a doron kasa”

Shugaban Hukumar Abincin ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya fadakar da cewa miliyoyin mutane na kusa da fadawa cikin tsananin yunwa sabili da matsalolin rikice-rikice, sauyin yanayi da Covid-19.

Shugaban (WFP) ya yi kira ga kasashen dake bayar da tallafi da kuma masu hannu da shuni da su taimaka kwarai da gaske domin magance matsalar yunwa a doron kasa.

Shugaban shirin abinci ta Majalisar Dinkin Duniya David Beasley ya shaidawa Kwamitin Tsaron MDD da cewa kasancewar yadda aka dauki mataki akan fadakarwar da ya yi na yiwuwar ‘annobar yunwa’ ya kare mutuwar miliyoyin mutane cikin watanni biyar da suka gabata.

Ya kara da cewa Hukumar WFP na iya kokarinta wajen ganin hanunta ya kai ga mutane miliyan 138 a wannan shekarar domin magance masu matsalar rashin abinci. Wannan dai shi ne mafi yawan mutanen da hukumar zata taimakawa a tarihi.


News Source:   ()