A yayin da ta ke sanar da yarjejeniya ta ƙurarren lokaci da aka cimma tsakanin Mexico da Amurka a kan tsaurara matakan daƙile kwararar baƙi ba bisa ƙa’ida ba, shugaba Sheinbaum ta ce an riga an fara aikewa da dakaru.
A ranar Asabar shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da matakan haraji masu nauyi a kan manyan abokan hulɗar ƙasarsa ta fannin kasuwanci, Canada, China da Mexico.
Makwaftanta na ƙut-da-ƙut, Canada da Mexico za su biya harajin kashi 25 a kan kayayyakin da su ke aikewa Amurka, kamar yadda shugaban ya bayyana, a yayin da China za ta biya ƙarin kashi 10 a kan kayayyakinta.
Canada da Mexico sun sanar da haraji a kan Amurka a matsayin martani, amma daga bisani sshugabannin ƙasashen su ka cimma yarjejeniya da Trump a ranar Litinin, wadda ta sa ya jinkirta harajin da wata guda.
Shugaba Sheinbaum ta ce an haɗa sojojin da za su yi tsaron kan iyakar ne daga sassan Mexico da ba a samun ƙalubalen tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI