Shugabar Gwamnatin jamus Angela Merkel ta taya murna ga likitocin da suka samar da riga-kafin cutar Corona (Covid-19) Dakta Ozlem Tureci da Farfesa Ugur Sahin.
Merkel ta kira Tureci da Sahin da suke mamallakan kamfanin BioNTech ta sadarwar bidiyo, inda ta ce tana matukar alfahari yadda a Jamus aka samar da wannan riga-kafin mai muhimmanci, ta kuma ce asalinsu Turkawa ne.
Sahin da Tureci sun godewa gwamnatin Tarayyar Jamus bisa taimakon da ta bawa aiyukansu.