An gano cewar kaso 1 cikin 3 na mutanen da suke kamuwa da cutar Corona tare da warkewa, a cikin watanni 5 bayan sallamar su daga asibiti, suna komawa tare da yin korafin ciwon numfashi da zuciya.
Hukumar Kididdiga ta Ingila, karkashin aiyukan jami'o'in University College London da Leicester suka gudanar, ta bibiyi mutane dubu 47,780 da suka warke daga Corona.
A binciken da aka gudanar an gano kusan kaso 30 cikin 100 na wadanda suka warke daga Corona, sun koma asibiti a cikin kwanaki 140 bayan sallamar su, inda aka fahimci suna da ciwon zuciya, matsalar numfashi da ciwon sukari, kuma kaso 23 na wadannan mutane sun rasa rayukansu.
Har yanzu ba a buga sakamakon wannan bincike a wata mujalla ta kimiyya ba, amma matsakaicin shekarun wadanda aka yi binciken a kansu shi ne 65, kuma sun kasance wadanda aka sallama daga asibiti a watanni 8 na farkon 2020 bayan warkewa daga cutar Corona.