MDD za ta binciki take hakkin bil adama da Isra’ila ta aikata a Gaza

MDD za ta binciki take hakkin bil adama da Isra’ila ta aikata a Gaza

Kwamitin Kare Hakkin Dan-Adam na Majalisar Dinkin Duniya a ya zartar da wani kuduri wanda ya hada da hanzarta kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa na kasa da kasa don bincikar take hakkin dan Adam da Isra'ila ta aikata a Gaza.

Zaman taro na musamman na majalisar, wanda aka kira don tattaunawa kan "mawuyacin halin da ake ciki game da hakkin dan adam" a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, an kammala shi tare da kaddamar da  kudurin da mai kula da kodinetan kungiyar Hadin Kan Musulunci (OIC) a Pakistan da Falasdinu ya gabatar.

Majalisar ta "yanke shawarar hanzarta kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa, na kasa da kasa, wanda Shugaban Kwamitin Kare Hakkin Dan-Adam ya nada, don yin bincike a yankin Falasdinawa da aka mamaye, ciki har da gabashin Kudus, da kuma a Isra'ila."

Kwamitin zai binciki "duk zargin da ake yi na take hakkin bil adama na kasa da kasa da duk keta haddi da cin zarafin dokokin kare hakkin dan adam na kasa da kasa tun daga ranar 13 ga watan Afrilu, 2021, da kuma duk wasu dalilan da ke haifar da rikice-rikice, gami da nuna wariyan launin fata, na addini da danniya,  kabilanci da makamantansu"

Kudurin ya yi kira ga dukkan kasashe da hukumomin kasa da kasa, da sauran masu hannu da shuni da su hanzarta tattara taimakon jin kai ga fararen hula ‘yan Falasdinu da ke Yankin Falasdinawa, ciki har da Gabashin Kudus.

Kudurin ya samu amincewar ne da kuri’u 24, inda kasashe 9 suka kada kuri’ar kin amincewa yayin da 14 suka kaurace.

Kasashen da suka kada kuri’ar kin amincewa sun hada da Austria, Czech Republic, Hungary, Germany, Malawi, Birtaniya, da kuma Uruguay, suna masu cewa wannan zai zama binciken da ba a taba yin irinsa ba.


News Source:   ()