Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, za ta goyi bayan Shirin Kare Hakkokin Dan Adam da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fitar wanda ya ce kasarsa za ta aiki da shi.
A ranar 2 ga Maris ne Shugaba Erdogan yayin wani taro a Fadar gwamnati a Ankara ya bayyana Shirinsu na Kare Hakkokin Dan Adam.
Kakakin kwamitin Kare Hakkokin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Liz Throssel ya ce,
"A shirye mu ke mu goyawa Turkiyya baya wajen ganin ta kare matsayin kasa da kasa."