An bayyana cewa sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 55 a Yammacin Kogin Jordan daga watan Janairu zuwa 23 ga Agusta, kuma ta tilastawa Falasdinawa 881 yin hijira sanadiyar lalata gidajensu a Gabashin Kudus.
A cikin rahoton da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya, an lura cewa an kori Falasdinawa 733 sanadiyar rushe musu gidaje 527 a yankin Yammacin Kogin Jordan na C, 148 sakamakon rushe musu gidaje 97 a gabashin Kudus akan dalilin cewa wai gidajen "ba su da lasisi"
A cikin tsarin "Yarjejeniyar Oslo ta Biyu" da aka rattabawa hannu tsakanin Falasdinu da Isra'ila a shekarar 1995, Yammacin Kogin Jordan; An raba shi zuwa yankuna A, B, da C.
An baiwa Falasdin ikon samar da tsaro da gudanarwar yankin "A zone", wanda ya kunshi kashi 18 cikin darin yankin, gudanarwar yankin "B zone" wanda ya kunshi kashi 21 cikin darin yankin an mikashi ga Falasdin inda aka mika kula da tsaronsa ga Isra'ila; tsaro da gudanarwar yankin C kuwa an mikashi ne ga Isra'ila.
Sau da yawa gwamnatin Isra’ila ba ta barin Falasdinawa su gina sabbin gine -gine ko fadadawa a cikin “zone C”, bisa dalilin cewa tana karkashin ikonta.