MDD ta yi kira ga Turkiyya da Girka su zauna teburin sulhu

MDD ta yi kira ga Turkiyya da Girka su zauna teburin sulhu

Majalisar Dinkin Duniya MDD ta yi kira ga Turkiyya da Girka dasu zauna akan teburin sulhu domin samar da sukuni a yankin Gabashin Bahar Rum.

Mai magana da yawun sakatare janar na MDD Stephane Dujarric a jawabin da ya yiwa manema labarai ya bayyana cewa muna matukar damuwa game da rikicin dake tsakanin Turkiyya da Girka.

Ya bayyana cewar babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa akwai babban bukatar bin hanyar lumana domin kawo karshen rikicin, inda kuma ya yi kira ga Turkiyya da Girka dasu tattauna da juna domin kwantar da hankula a yankin.

Dujarric, ya kara da cewa sakatare janar na MDD ya yi alkawarin bayar da gudunmowa domin bin hanyar diflomasiyya akan kwantar da hankula da kuma kawo karshen rikicin yankin.

 


News Source:   ()