MDD ta yi kira ga Malaman Addini da su taka rawa wajen yaki da Corona

MDD ta yi kira ga Malaman Addini da su taka rawa wajen yaki da Corona

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga Malaman Addini da su taka muhimmiyar rawa wajen yaki da annobar Corona (Covid-19).

A wani sakon bidiyo da Guterres ya fitar ya godewa Shugabannin Addini bisa irin rawar da suke takawa wajen yaki da Corona amma ya bukaci da su kara kokarin da suke yi.

Guterres ya kara da cewar ya yi kira ga Malaman Addini d su soki yadda ake nuna wariya da kyama ga masu dauke da cutar, da ma yadda ake zaluntar mata.

Haka zalika ya bkaci da a aiwatar da ka'aidojin da Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar game da taruwa a wuraren Ibada.

Sakatare Janar na MDD ya tunatar da cewar annobar ta janyo an dakatar da karatun miliyoyin dalibai, a saboda haka ya bukaci Malaman Addini da su bayar da gudunmowa wajen neman mafita.


News Source:   www.trt.net.tr