MDD ta yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da yunkurin gina gidaje a Falasdin

MDD ta yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da yunkurin gina gidaje a Falasdin

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta yi kira ga Isra'ila da ta "dakatar da gina sabbin gidaje 5,000 da zata yi ba bisa ka'ida ba a Falasdinu"

Kodinatan Mjalisar Dinkin Duniya akan harkokin zaman lafioya a Gabas ta Tsakiya Nickolay Mladenov, ya fitar da wata sanarwa a rubuce inda yake cewa Isra'ila a ranar 14 da 15 ga watan Oktoba ta amince da gina gidaje dubu 5, sai dai gina gidajen a gurin da ta bayyana mataki ne da ya sabawa dokar kasa da kasa.

Mladenov ya kara da cewa wannan matakin zai kasance babban abinda zai dakile yunkuirin zaman lafiyar yankin kuma zai kawo cikas ga yunkurin samar da kasa biyu tsakanin Isra'ila da Falasdin, inda ya kara da kira ga shugabanin Isra'ila da su dakatar da wannan yunkurin nan take.

 


News Source:   ()