Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa matuka akan kifar da gwamnatin farar hula da aka yi ranar Alhamis a Myanmar tare da daure shugabanin siyasa da na kungiyoyi masu zaman kansu.
Majalisar ta bayyana cewa tsare jagoran kasar Aung San Suu Kyi da kuma shugaban kasar Win Myint ya sabawa doka. Inda kuma ta yi kira da a gaggauta sakesu da kuma mayar da mulki ga hannun farar hula.
Mamabobin majalisar sun bayyana nuna goyon bayansu akan mayar da mulki ga hannaun farar a kasar ta Myanmar tare da kira da a karfafa ma’aikatun siyasa, kare hakkokin bil adama da kuma inganta da bin dokar kasa.