MDD ta kyamaci harin da Armenia ta kaiwa farar hula a Ganja

MDD ta kyamaci harin da Armenia ta kaiwa farar hula a Ganja

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta kyamaci harin roka da Armenia ta kai a yankin farar hula a kasar Azerbaijan da ya yi sanadiyar rasa rayuka.

MDD ta bayyana bakin cikin samun labarin harin da Armenia ke kaiwa a yankin farar hula a Ganja dake Azerbaijan. 

Mai magana da yawun sakataren Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Anadolu  da cewa sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres na damuwa matuka akan rikicin dake ci gaba da afkuwa tsakanin kasashen biyu.

Guterres ya tattauna da ministan harkokin wajen Armenia Zohrab Mnatsakanyan da na Azerbaijan  Ceyhun Bayramov ta wayar tarho inda ya yi kira ga dukkanin bangarori su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta su koma teburin sulhun.

Haq dake bayyana cewa rikicin na makonni uku ya taba farar hula inda ya kara da cewa muna masu matukar kyamatar harin da aka kaiwa yankin farar hula. 

Mai gabatar da kara na kasar Azerbaijan ya bayyana cewa a wani harin da Armenia ta kai a yankin farar hula a Ganja mutun 12 suka rasa rayukansu inda wasu 40 suka jikkata. 


News Source:   ()