MDD ta koka kan rashin warware rikicin siyasar Libya

MDD ta koka kan rashin warware rikicin siyasar Libya

Jakadan majalisar ɗinkin duniya a Libya, Taher Al-Sunni ya shaidawa zaman kwamitin tsaro na majalisar cewa halin da ake ciki a ƙasar na matuƙar ɗaure kai musamman a watanni biyun da suka gabata, ta yadda ake ganin farraƙa a dukkanin ɓangarorin da suka shafi siyasa tattalin arziki da ma yunƙurin tabbatar da tsaro a ƙasar ta yankin Magreb a nahiyar Afrika.

A cewar Al-Sunni halin da ake ciki a ƙasar ya sanya shakku a fatan da ake da shi na cimma jituwa tsakanin ɓangarorin da ke mulkin ƙasar a Tripoli da Benghazi.

Sabuwar ɓaraka 

Cikin watanni biyu da suka gabata, an samu ɓaraka mai girma tsakanin ɓangarorin biyu wadda ke ci gaba da tsananta kama daga fannonin siyasar tattalin arziki da kuma tsaro lamarin da ya yi mi’ara koma baya ga yunƙuri ƙasashe na samar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasar wadda ta shafe tsawon shekaru ta na fuskantar yaƙin basasa.

Taher Al-Sunni ya shaidawa kwamitin cewa hanya ɗaya ta warware rikicin Libya bai wuce gudanar da sahihin zaɓe ba.

Rikicin baya-bayan nan da ɓangarorin biyu suka samu farraƙa akai shi ne korar gwamnan babban bankin ƙasar Sadiq al-Kabir da gwamnatin Tripoli ta yi da nufin maye gurbinsa da wani ko da ya ke an bayyana matakin a matsayin wanda ya saɓawa doka.

Libya ta faɗa yaƙin basasa ne tun bayan da NATO ta jagoranci tawagar Sojin ƙasashe wajen yaƙar Moammar Gadhafi a shekarar 2011, shugaba mafi daɗewa a kujerar mulki a tarihin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)