A cewar alkalumman da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar yau litinin 19 ga watan nan na Augusta, fiye da rabin adadin ma’aikatan agajin da suka mutu a shekara 2023 da ta gabata an kashe su ne yayin yakin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin kungiyar Hamas da Isra’ila a watanin ukun farkon shekarar ta hanyar hare-haren da aka kai ta sama.
Yayin da Sudan ta kudu wadda yakin basasa da rikicin ƙabilanci suka ɗaiɗaita da kuma Sudan inda yakin da ya faro tun a cikin watan Afrilun 2023 tsakanin manyan janarorin sojin ƙasar biyu da ke gaba da juna, wanda majalisar ta ce su ke a matsayi na biyu da na uku da ke da yawan ma’ikatan agajin da aka kashe.
Sauran kasashe 10 inda ma’aikatan agajin suka fi rasa rayukan su, sun hada da Isra’ila da Syria da Habasha da Ukraine da kuma Somalia baya ga Jamhuriya Dimokradiyar Congo da kuma Bama.
Ta cikin wani gargadi da ta fitar, Majalisa Ɗinkin Duniya tayi hasashen cewa adadin jami'an da ake kashe mata ka iya zarta na ma’aikatan agaji 280 da aka gani a bana idan har rikice rikicen da duniya ke gani ya ci gaba da ta'azzara a wannan shekara ta 2024.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI